Najeriya: Harin Amurka ne mafitar Tsaro?
December 26, 2025
Najeriya da kasar ta Amurka dai sun ce, sun hada hannu da nufin kai harin da ke da babban burin kisan 'yan kungiyar ISIS da ke yankin yanzu. To sai dai kuma daga dukkan alamu, harin yana shirin barin baya da kura cikin kasar da ke masa kallo na dabam, duk da cewar sun kira batu na kare ta'adda kuma sun ce harin ya samu amincewar gwamnatin Tarayyar Najeriya.
Kama daga burinsa zuwa dabarar kai shi da ma uwa uba garin na Sakkwato dai, daga dukkan alamu shugaban na Amurka da kila ma fadar gwamnatin Tarayyar Najeriya suna da tambayoyin amsawa bisa harin na ranar Kirsimeti. Najeriyar dai a fadar ministan harkokin wajenta Yusuf Tuggar ita ta bayar da bayanan sirri, na harin bayan wata tattaunawar wayar tarho da ta kai tsawon mintuna 19 a jiya, kuma ta kai ga amincewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Bin kowacce hanya domin yaki da ta'adanci a Najeriya?
Majiyoyin sojan Tarayyar Najeriyar sun ce, an kai harin ne bisa bayannan sirrin da ke fadin masu ta'addar ISIS daga Mali da Burkina faso, na shirin su kai hari cikin yankin na Sakkwato da Kebbi da Zamfara da ma jihar Katsina. Abdul Aziz Abdul Aziz dai na zaman mai taimakawa shugaban kasar a fannin yada labarai, kuma ya ce: "Harin na zaman dan ba, a kokarin kare ta'addar a ko'ina a Tarayyar Najeriyar.
To sai dai kuma ko ya zuwa ina dabarar aikin tare ke shirin ta kai a kokarin kare ta'addar, zabin kauyen Jabo da ke a Sakkwato daga dukkan alamu ya saba da tunanin kai farmaki cikin tungar ISIS ta ta'adda. Muni Fara Girke dai na sharhi cikin batun tsaron a jihohin na Sakkwato da Kebbi da Zamfara, kuma ya ce: "Ba tarihin ISIS, a cikin yankin da ya dauki hankalin na Amurka."
Yakar 'yan ta'adda ko kokarin burge Amurka?
Duk da cewar dai rahotannin da ke fitowa daga yankin sun ce, babu asarar rayuka sakamakon harin dai, ga dukkan alamu tana kara fitowa fili gwamnatin ta Abuja na dada daure wando, a kokarin burge Amurka da kila neman kauce wa fushin Shugaba Donald Trump tare da kila jefa daukacin makomar kasar cikin yanayin da ba shi da tabbas.
Can a Venezuela dai alal ga misali kokarin kare kwaya a bangaren na Amurka ne dai ya rikide ya zuwa neman sauyi, na gwamnatin da ke a birnin Caracas yanzu haka. Kuma ko a nan a Najeriya dai, a tunanin Dakta Umar Ardo da ke zaman kwarrare a bangaren soja, kai harin na Amurka na da burin da ya zarta kokarin kare ta'adda.