Harin Bam a zaben 'yan Majalisun Dokokin Pakistan
May 11, 2013A wanna Asabar din ce al'ummar kasar Pakistan ke kada kuri'unsu domin zaben 'yan majalisar da zasu wakilce su. Wannan zaben dai shine zai kasance zakaran gwajin dafi, na sauyin mulki daga sojoji da suka mulki kasar na tsawon lokaci zuwa hannun farar hula. Wadanda suka cancanci zabe miliyan 86 ne dai ake saran za su kada kuri'un nasu a rumfunan zabe dubu 70 dake sassan kasar, domin zaben wakilai da zasu haye kujerun majalisar 272. To sai dai fargabar rigingimu na cigaba da yin dandazo ga zaben na Pakistan. Tuni dai aka dauki tsauraran matakan tsaro da jami'an 'yan sanda dana soji sama da dubu 600. Kusan mutane 130 ne dai kawo yanzu suka rasa rayukansu, a hare haren da aka kai gabanin zaben. Ko da safiyar yau sai aka samu tashin bama bamai a birnin Karaci, wanda ya kashe mutane 11 tare da raunata wasu masu yawa. Jam'iyyun tsohon Firaministan Nawaz Sheriff da ta fitattcen dan wasan motsa jiki na Pakistan Imran Khan ne dai ake hasashen zasu fafata wajen neman kujeru mafi rinjaye a Majalisar kasar.
Mawallafiya : Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Yahouza Sadissou Madobi