1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaPakistan

Pakistan: Harin bam ya halaka mutane

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 29, 2023

Rahotanni daga Pakistan na nuni da cewa harin bam da aka kai a kusa da wani Masallaci yayin da ake jerin gwanon bikin maulidi, ya halaka mutane sama da 50 ciki har da wani babban jami'in gwamnati.

Pakistan | hari | Masallaci | Maulidi | Mastung | IS | Taliban
Waadanda harin ya rutsa da su na karbar magani a yankin na MastungHoto: District Police Office/AP Photo/picture alliance

Jami'an gwamnati da na 'yan sanda sun tabbatar da da cewa harin da ya afku a gundumar Mastung da ke lardin Baluchistan yayin da mutane kimanin 500 suka taru domin yin murnar bikin zagayowar ranar da aka haifi Annabi Muhammad (SAAW), ya kuma raunata kimanin mutane 70. Musulmi kan yi gangami a wannan rana da aka fi sani da ta Maulud an-Nabi, tare da raba abinci kyauta ga mutane. Kawo yanzu dai babu wani ko wata kungiya da ta dauki nauyin harin, amma lardin na Baluchistan ya sha fuskantar hare-hare daga tsageru da masu dauke da makamai da ke kai hari kan jami'an tsaro da kuma 'yan kungiyar Taliban ta Pakistan da ke kai hari a wuraren ibada da kuma 'yan kungiyar IS da suka sha yin ikirarin kai hare-hare a sassa da dama na lardin.