Harin Bam ya halaka rayuka a Najeriya
October 30, 2017Rahotanni daga Najeriya na cewa wani dan kunar bakin wake ya halaka mutane akalla 5 tare da jikkata wasu da dama, a wani hari da ya kai kauyen Ajiri Yala da ke arewacin birnin Maiduguri na jihar Borno. Kamar dai yadda wani dan Kato-da-Gora ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP, maharin ya saje ne da masallata cikin wani masallaci yayin sallar Asuba. Ko a Lahadin da ta gabata ma wani dan Kato-da-Goran ya rasa ransa a wani shingen binciken da ke yankin Muna a birnin Maiduguri, lokacin da wasu 'yan mata masu bama-bamai suka tarwatsa kansu.
Wasu bayanan da ke fitowa daga yankin Gulak na karamar hukumar Madagali a arewacin jihar Adamawa ma dai na cewa wasu 'yan matan biyu da aka yi zargin sun fito ne daga sansanin Sambisa, sun tarwatsa kansu a kauyen Dar, sai dai babu labarin mutuwar wani ko samun rauni.