Harin bam ya hallaka sojojin Masar bakwai
October 19, 2014Talla
Wani bam da aka dana a gefen hanya ya hallaka sojojin kasar Masar bakwai, tare da jikata wasu hudu cikin yankin Sinai mai fama da tashe-tashen hankula.
Jami'ai sun ce bam ya tarwatse lokacin da motocin yakin sojoji ke wucewa, wadanda ke sintirin aikin tsaro na bututun gas. Ana samun tashin hankali a yankin na arewacin Sinai da ake dangantawa da masu kaifin kishin addinin Islama.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe