Harin bam ya hallaka 'yan sanda a Kenya
May 24, 2017'Yan sandan na bisa hanyar su ce ta zuwa birnin Garisa lokacin da abun da ake zaton bam ne ya tashi kusa da wani ofishinsu na bincike na kan iyaka na Liboi, inda nan take su uku suka mutu bayan da motar da suke ciki ta taka bam din da aka dana. Babu dai wani da ya dauki alhakin kai wannan hari, amma kuma sanin kowa ne kasar ta Kenya na fama da iri-irin wannan matsala ta hare-hare musamman ma daga 'yan jihadi na kungiyar Al-Shebaab da ke da alaka da kungiyar Al-Qaida.
Tun dai lokacin da take samar da sojoji wajen yakar 'yan jihadi a Kudancin Somaliya, kasar ta Kenya ke fusknatar hare-hare daga 'yan kungiyar wanda mafi muni su na cibiyar kasuwanci ta Westgate da ke birnin Nairobi da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 67 da kuma na jami'ar garisa da ya shafi mutane 148.