1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bam ya kashe mutane a Libiya

Abdul-raheem Hassan
May 25, 2018

Jami'an tsaro sun tabbatar da harin da aka kai cikin mota a tsakiyar birnin Benghazi, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 7 yayin da wasu kusan 20 suka jikkata.

Libyen Straßenkämpfe zwischen Armee und Ansar al-Scharia Milizen in Benghasi
Hoto: picture alliance/abaca/M. Elshaiky

Hukumomin tsaro sun ce bam din ya tashi ne cikin wata mota kusa da babban Otal din Tibesti, inda musulmai ke gangamin bukukuwan murna a watan azumin Ramadana. Babu wata kungiya da ta dau alhakin harin, amma hukumomin Libiya na zargin 'yan ta'adda da aka ci karfinsu a yankin ne ke yunkurin maida martani. A baya dai sojoji sun sanar da nasarar kakkabe tungar kungiyoyin ta'adda da ke birnin na Benghazi, tare da ayyana karbe iko da birnin bayan shafe shekaru uku ana gwabza fada.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW