1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin bam ya kashe mutane da dama a Pakistan

June 20, 2026

A kalla mutane bakwai ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da wasu uku suka jikkata a wasu hare-haren bama-bamai a arewa maso yammacin Pakistan.

Jami'an soji na aikin ceton mutane bayan wani harin bam a Pakistan
Hoto: Arshad Butt/AP Photo/picture alliance

Babu wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin kai tagwayen hare-haren a arewa maso yammacin Pakistan, sai dai hukumomi na cewa suna gudanar da bincike domin gano wadanda suke da hannu a harin.

Rahotanni sun yi nuni da cewa an kai harin farko ne a kan wata mota, yayin da daya harin aka kai unguwar Bannu. A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, shugaban kasar Pakistan Asif ​Ali ⁠Zardari, ya yi Allah wadai da harin tare da yin gargadi ga masu goyon bayan ayyukan ta'addanci na cikin gida da na waje da ma su taimaka musu da kudade da kuma hanyoyin sadarwa.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW