Harin bam ya kashe mutun 17 a Maiduguri
January 14, 2014Talla
Bam ɗin ya tarwatse ne a tsakiyar 'yan kasuwa masu saye da sayar wa kusa da wani offishin a dai dai lokacin da wata mota cike da itace ke ficewa .Wannan labari ya fito ne daga shugaban 'yan sandar jihar ta Borno Lawan Tanko.
A cewar wani ɗan kasuwar da ya gane wa idanunsa, ya ce wasu da ba'a san ko su wanene ba, suka naɗe bam ɗin cikin wani bahu kuma suka yada shi kusa da masu nama, a kasuwar Jagwal.Shi ma wani da ya gane wa idanunsa, cewa yake nan take ya ga kusan mutun 20 a kwance , sai dai ba shi da tabbacin ko dukka sun mutu. Bam ɗin ya fashe ne a dai dai lokacin da ake yin bukukuwan Maulid
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Abdourahamane Hassane