1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin bam ya sake salwantar da rayuka a Siriya

March 18, 2012

Wuni guda bayan harin tagwayen bama-baman da ya firgita Siriya, an sake kai wani harin a cikin wata karamar mota a birnin Aleppo

epa03100160 Syrian security forces gather in front a damaged building at a security compound which was attacked by an explosion, in Aleppo, Syria, 10 February 2012. According to syrian news agency at least 28 people were killed and 175 injured in two explosions that targeted security compounds in Syria's second largest city, Aleppo, state television reported. The two blasts were the first to hit Aleppo, which has witnessed relative calm since the uprising against the Syrian president Bashar al-Assad started in mid-March. EPA/STR
Hoto: picture-alliance/dpa

Gidan talibijin na kasar Siriya ya rawaito cewa wata karamar mota dankare da bama-bamai ta fashe a wata unguwa da ke birnin Aleppo a wannan lahadin, wuni guda bayan da wasu tagwayen bama-bamai suka fashe a babban birnin kasar wato Damascus.

Majiyoyin adawa sun ce harin ya shafi wani yanki da ke kusa da wani ofishin jami'an tsaro. Wakilan kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch wadanda ke sanya ido a yadda alamaura ke gudana a Siriyar sun ce harin ya salwantar da rayuka kuma da dama sun yi rauni, to sai dai basu bada adadin wadanda abun ya shafa ba. Harin na ranar lahadi, shine harin kunar bakin wake na biyar, wanda aka kai a karamar mota tun bayan da aka fara nuna adawa da mulkin shugaba Bashar Al-Assad na tsawon shekara guda yanzu.

Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Zainab Mohammed Abubakar