1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaUkraine

Rasha ta halaka mutane 16 a Ukraine

September 6, 2023

Dakarun Rasha sun kai kazamin hari a wata kasuwa da ke Gabashin Ukraine inda suka halaka mutane da dama tare da jikkata wadansu.

Rasha ta halaka mutane 16 a Ukraine Hoto: Valentyn Ogirenko/REUTERS

Akalla mutane 16 sun bakunci lahira sanan wasu 31 suka jikkata a yayin harin da dakarun Rasha suka kai a wata kasuwa da ke a nisan kilomita 30 da birnin Bakhmut da ke Gabashin Ukraine inda aka kwashe sama da shekara guda ana gwabza fada.

Karin bayani: Zafafa harin Rasha a Ukraine

Wannan hari na zuwa ne a daidai lokacin da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ke ziyarar ba zata a birnin Kiev fadar gwamnatin Ukraine inda zai sanar da sabon tallafi wa kasar domin fuskantar mamayar Rasha.

Karin bayani: Amurka za ta bai wa Ukraine sabon tallafi

Dama dai a lokacin da aka sanar da ziyarar da mista Blinken a safiyar yau, Rasha ta zargin Amurka da fakewa da sunan Ukraine domin yin yaki da ita, inda ta ce duk wani tallafi da Washington za ta bai wa Kiev ba zai kawo mata cikas ba kan burinta a kan Ukraine.