1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin bama-bamai a Bagadaza ya halaka aƙalla mutane 75

January 22, 2007

Akalla mutane 75 sun rasu sannan sama da 150 sun samu raunuka sakamakon wasu tagwayen hare haren bam da aka kai da mota a wata kasuwar sayar da gwanjo dake tsakiyar birnin Bagadaza. Harin dai shi ne mafi muni tun bayan wasu tagwayen hare hare da aka kai a wajen harabar jami´ar Bagadaza wanda ya halaka mutane 70 kwanaki 6 da suka wuce. Wadannan tashe tashen hankula sun zo bayan isar rukunin farko na dakarun da shugaban Amirka GWB yayi alkawarin turawa a Iraqi. Sama da sojoji dubu 3 suka isa a Bagadaza don fara aiki a ranar daya ga watan fabrairu.