SiyasaJamus
Harin Boko Haram ya kashe sojojin Kamaru
July 25, 2021Talla
Rahotannin da ke fitowa daga Kamaru, na cewa wani harin mayakan Boko Haram ya salwantar da sojojin kasar akalla shida a ranar Asabar.
Maharan sun kuma jikkata karin wasu sojojin Kamaru da dama tare da yin awon gaba da makamansu.
Gwamnan yankin arewa mai nisa inda lamarin ya faru, shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin ta kafar watsa labarun cikin gida.
Hukumomin na Kamaru, sun yi bakin cikin rashin zaratan mayakan kasar a harin na Boko Haram a yankin Fotokol iyaka da Najeriya
Sun kuma jinjina wa sadaukar da rayuwarsu da sojojin suka yi saboda kasa.
Wani rahoton da 'yan sanda suka fitar, ya yi nunin cewa dakarun na Kamaru takwas ne suka mutu a harin, kamar yadda wasu majiyoyi ma suka tabbatar.