Harin cocin Katolika na Istanbul ya yi sanadin mutuwa daya
January 28, 2024Wasu mahara guda biyu da suka rufe fuskarsu sun bude wuta a kan wani mutum da suka kashe har lahira, a tsakiyar cocin Katolika da ke Istanbul, kafin daga bisani su ranta a na kare. Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya jajanta wa iyalan wanda ya rasa ransa tare da bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta dauki matakan da suka dace don cafko maharan a duk inda suke. Shi kuwa shugaban darikar roman katolika ta duniya Paparoma Francis ya yi Allah-wadai da harin tare kuma bayyana kusancinsa da al'ummar wannan cocin.
Harin dai ya faru ne da hantsi a cocin Santa Maria da ke gundumar Sariyer na Istanbul, a cewar ministan cikin gidan kasar Turkiyya Ali Yerlikaya a lokacin da ya yi amfani da shafukan sada zumunta wajen bayyana cewa an bude bincike. sai dai wannan harin ya zo ne mako guda bayan ganawa da Erdogan ya yi da firanministar Italiya Giorgio Meloni