Harin da Amirka ta kai Somalia bai cimma manufa ba
January 11, 2007Talla
Farmakin da jiragen saman yakin Amirka suka kai a Somalia bai yin nasarar kashe wasu mutane 3 da ake zargin cewa kusoshin kungiyar al-Qaida ne ba. Wani babban jami´in Amirka da ya ki a bayyana sunansa ya fada a yau alhamis cewa har yanzu suna neman ´yan ta´addan. A ranar litinin da ta gabata Amirka ta kai hari akan wani kauye dake kudaancin Somalia a wani yunkuri na kashe wasu ´yan Al´Qaida da ta ke zargi da hannu a hare haren da aka kai kan ofisoshin jakadancin ta guda biyu a 1998 da kuma wani hari da aka kai kan wani otel mallakar Isra´ila a shekara ta 2002.