SiyasaTurai
Harin da Rasha ta kai wa Ukraine cikin dare ya halaka mutane
February 9, 2026
Talla
Ukraine ta tabbatar da cewa hare-haren da Rasha ta kai ma ta cikin dare zuwa wayewar garin Litinin, sun halaka mutane uku a garuruwan Odesa da Kharkiv.
Babban jami'in sojin Ukraine a Odesa Sergiy Lysak, ya ce Rasha ta yi amfani da jirage marasa matuka kirar kasar Iran, wajen kai wannan farmaki, wanda ya lalata gidaje da bututan iskar gas.
Karin bayani : Amurka na son a kawo karshen yakin Ukraine a Yuni
Rasha na ci gaba yi wa makwabciyar ta ta Ukraine ruwan bama-bamai, yayin da a gefe guda kuma take tattaunawar samar da zaman lafiya domin kawo karshen yakin na tsawon shekaru hudu, bisa matsin lambar Amurka.