1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin dan bindiga a wata makaranta a Rasha

Abdullahi Tanko Bala
September 26, 2022

Wani dan bindiga ya kai hari wata makaranta a Rasha inda ya kashe gwamman mutane ciki har da kananan yara

Russland I Schießerei an einer Schule in Izhevsk
Hoto: picture alliance/dpa/TASS

Yawan mutanen da suka rasu a harin dan bindiga a wata makaranta a Rasha ya kai mutum 15 ciki har da kananan yara bakwai yayin da wasu mutanen 25 suka sami raunuka.

Rahotanni sun ce dan bindigar tsohon dalibi ne a makarantar da ke tsakiya Rasha.

Harin shi ne na baya bayan nan da ake kaiwa da bindiga a makarantu wanda ya rikita Rasha a  'yan shekarun da suka wuce.

Wannan dai na zuwa ne yayin da kasar ke gangamin daukar dubban maza domin yaki a kasar Ukraine.

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi Allah wadai da harin wanda ya ce ya nuna tsantsan rashin imani.