1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Harin Bahar Aswad ya dakatar da aikin kamfanin Jamus

January 12, 2024

Kamfanin da ke sarrafa motocin da ke amfani da lantarki na Tesla ya sanar da dakatar da ayyukan sa na wani dan lokaci, sakamakon farmakin da 'yan fashin teku ke kaiwa bahar aswad.

Hukumomin kamfanin sun dauki wannan mataki ne na dakatar da ayyukan kamfanin da ke birnin Berlin na kasar Jamus, tun daga 29 ga watan nan na Janairu  har zuwa 11 ga watan Fabrairu 2024, sakamakon karancin sinadaran sarrafa motocin da ake fama da ita kasancewar ta tekun Bahar Aswad ake shigo da kayayyakin, kuma yankin tekun na cikin tashin hankali sakamakon mayakan Houthi na Yeman da ke kokarin karbe iko da yankin a wani mataki na nuna goyon baya ga mayakan Hamas a yakin da ta ke yi da Isra'ila.

Kamfanin na Amurka da ke kera motocin masu amfani da lantarki na daga cikin manyan kamfanonin da suka fara daukar wannan mataki na katse ayyukansu sakamakon tsaikon jjigilar kayayyakin a tekun Bahar Aswad.

Kamfanoni da dama irin su Geely, kamfani na biyu mafi girma a Chaina da kamfanin sarrafa kayan gado da kujeru na kawa na kasar Sweden wato IKEA sun sanar da cewa suna fuskantar tsaiko wajen shigo da kayayyaki ta teku.

Harin na mayakan Houthi na kasar Yeman masu dauke da makamai ya haifar da cinkoso akan mashigin  Suez Canal, da ke kasancewa hanya mafi sauri wajen shigar da kaya yankin Asiya da Turai.