1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Harin Isra'ila ta sama ya halaka mutane 13 a Lebanon

Suleiman Babayo LMJ
June 10, 2026

Harin Isra'ila ta sama ya halaka mutane 13 a yankin kudancin Lebanon.

Harin Isra'ila a Lebanon
Harin Isra'ila a LebanonHoto: Mohammed Zaatari/AP Photo/picture alliance

Wani harin sojojin sama na Isra'ila ya halaka mutane 13 a yankin kudancin Lebanon a wannan Laraba. Hukumomin tsaron Lebanon sun ce Isra'ila tana kara kaimi hare-hare kan mayakan kungiyar Hezbollah da ke samun goyon bayan kasar Iran.

Halin da ake ciki

Harin Isra'ila a LebanonHoto: Mohammed Zaatari/AP Photo/picture alliance

Zuwa yanzu imanin mutane 3,700 suka halaka sakamakon hare-haren Isra'ila a Lebanon tun farko watan Maris lokacin da fada ya doce, inda ma'aikatar kula da lafiya ta Lebanon ta ce kimanin wasu mutane milyan 1.2 sun tsere daga gidajensu, domin tserewa daga wuraren da ake fama da tashe-tahsen hankula tsakanin bangarorin na Isra'ila da mayakan Hezbollah.