1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Harin Isra'ila ya halaka mutane biyar a Lebanon

September 21, 2025

Isra'ila ta kai farmaki kan wasu mutane a kudancin Lebanon ta hanyar amfani da jirgi mara matuki, a cewar ma'aikatar lafiyar Lebanon.

Wata mota da Isra'ila ta kai wa hari a Lebanon
Wata mota da Isra'ila ta kai wa hari a LebanonHoto: Ramiz Dallah/Anadolu Agency/IMAGO

Kamfanin dillancin labarai na Lebanon ya rawaito cewa Isra'ila ta kai farmakin ne a kusa da Bint Jbeil da ke kudancin birnin Beirut. Isra'ila dai ta kaddamar da hare-hare kan Lebanon da sunan farautar mayakan Hezbollah, duk da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin kasashen biyu a watan Nuwambar 2024, domin kawo karshen tashin hankalin.

Karin bayani: Israila ta kai hari Beirut karon farko bayan tsagaita wuta

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Firaministan Lebanon Nawaf Salam ya ce da gangan Isra'ila ta kai farmakin kan fararen hula. Isra'ila dai ta zafafa hare-haren da take kai wa Lebanon a wannan mako.