Harin jirgi marar matuki ya haddasa gobara a Dubai
March 16, 2026
Tashin wuta a kusa da babban filin jirgin saman birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa a wannan Litinin, ya tilasta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na wucin-gadi, sanadiyyar harin jirgi marar matuki.
To sai dai babu rahoton asarar rai ko jikkata da aka samu bayan harin na filin jirgin saman Al Maktoum, mai matukar tasiri ga tattalin arzikin kasar, sanadiyyar hada-hadar matafiya, kamar yadda hukumomin Dubai suka wallafa a shafin X.
Karin bayani - Trump ya yi ikrarin tura jirage mashigin Hormuz
Tun bayan barkewar yakin Iran da kawancen Amurka da Isra'ila a ranar 28 ga watan Fabarairu, kimanin hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuka sama da dubu aka fuskanta a kasashen yankin Gulf, masu karfin arzikin man fetur, wadanda kuma ke da sansanonin sojin Amurka.
A sakon da ma'aikatar tsaron Hadaddiyar Daular Laraba ta wallafa a shafinta na X, ta ce garkuwar tsaro ta sararin samaniya ta samu nasarar kakkabo hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuka daga Iran.
Karin bayani - Trump na neman taimakon kasashen duniya don kare mashigin Hormuz
A wani labarin kuma ma'aikatar tsaron Saudi Arebiya ta sanar da harbo jirage marasa matuka 61 da aka harba mata cikin daren Lahadi zuwa wayewar garin Litinin, kamar yadda ta wallafa a shafin X.
Tuni shugaba Donald Trump na Amurka ya sanar da cewa akwai yiwuwar ya jinkirta ziyarsa ta zuwa China a karshen watan Maris, a kokarinsa na matsawa Beijing lamba domin ta taimaka wajen tursasa bude mashigin Hormuz da Iran ta datse, wanda ya haddasa tsadar man fetur a duniya.
Karin bayani - IEA: Yakin Iran ya janyo babbar tangarda ga man fetur a duniya
A tattaunawarsa da Financial Times ranar Lahadi, Mr Trump ya ce la'akari da yadda China ta dogara da mai daga Gabas ta Tsakiya, wajibi ne ta agazawa yunkurinsa na hada gangamin taron dangi domin bude Hormuz ta karfin tsiya.
Jawabin shugaban na zuwa a daidai lokacin da sakataren baitil-malin Amurka Scott Bessent ke shirin ganawa da mataimakin shugaban China He Lifeng a wannan Litinin a birnin Paris na Faransa, inda za su tattauna batutuwan da suka shafi kasuwanci.