Harin kunar bakin wake a Iraki
April 1, 2013Talla
Dan kunar bakin waken dai ya shiga cikin ginin karamar hukumar ne da wata motar dakon man fetur da ya ke tukawa wada ke damfare da bama-bamai inda bai yi wata-wata ba ya tada bam din.
Da ya ke karin haske game da harin, Kyaftin Mohammed Salihi na rundunar 'yansandan Tikrit wanda shi ma ya jikkata a harin, ya ce dan kunar bakin waken ya tada bam din ne lokacin da aka tsaida shi domin yin bincike a daura da ofishin 'yansada da ke cikin harabar.
Kawo yanzu dai ba wata kungiya da ta dauki kai harin. Irin wadannan hare-haren a Iraki dai sun karu tun bayan da yaki tsakin gwamnatin Assad da 'yan tawayen kasar ya ta'azzara.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman