Harin kunar bakin wake a Kamaru
November 28, 2018
Talla
Akalla mutane 29 suka jikkata yayin da wata 'yar kunar bakin wake ta tarwatsa kanta a garin Amchide dake yankin arewa mai nisa a iyakar Najeriya da Kamaru, yankin da ya yi fama da harin 'yan Boko Haram.
Rahotanni sun ce sojoji sun sami nasarar harbe 'yar kunar bakin wake ta biyu wadda ta yi kokarin tada nakiyar da take dauke da ita.
Wani jami'in tsaro a yankin da ya bukaci a sakaya sunansa yace an kai harin ne a ranar da ake cin kasuwa a garin a kuma lokacin da ake tsakiyar hada hadar kasuwanci.