Harin kunar bakin wake a Masar
October 24, 2014Talla
A cewar jami'an tsaron kasar ta Masar, harin ya faru ne a yankin arewa maso yammacin Al-Arich, yankin dake da tarin duwatsu bayan da matukin motar ya tashi bam din kusa da sojojin. A wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta masar ta fitar, tace a ayammacin yau din nan ne shugaba Abdel Fattah al-Sissi, yayi kiran wani taron gaggawa na majalisar tsaron kasar domin bi sau da kafa yadda lamarin yake a wannan yanki inda hadarin ya afku. Wannan dai shine babban hari mai muni da ya rutsa da sojoji masu yawa tun bayan hambare zabeben shugaban kasar Mohamed Morsi a watan Yuli na 2013.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Pinado Abdu Waba