Harin kunar bakin wake a Pakistan
November 22, 2012Talla
Wani harin kunnar bakin waken da aka kai a birnin Rawalpindi a Pakistan ya yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane 23 tare da raunata kimanin 62 a daren Laraba zuwa safiyar Alhamis din nan a wata sanarwar da hukumomin kasar suka bayar. Wannan harin na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ta Pakistan ke karbar bakuncin wani taron kasa da kasa da ya hada wasu kasashen musulmai 8 ciki har da Masar,Turkiya,da ma Iran da nufin tautauna batun bunkasa ci-gaban al'umma.
Jimlar adadin mutane 35 ne dai suka rasa rayukansu a hare hare daban daban da aka kai a fadin kasar a wannan Larabar wadanda kawo yanzu babu wani ko wata kungiyar da ta dauki alhakin kaisu.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Umaru Aliyu