1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Harin Magdeburg zai zama maudi'i a yakin neman zaben Jamus?

Pieper Oliver SB/MAB
December 23, 2024

'Yan siyasa sun saba amfani da irin harin da aka fuskanta a kasuwar Kirsimeti ta Magdeburg a Jamus, inda kimanin mutane biyar suka rasu. Wannan batun tsaron zai mamaye yakin neman zaben gama-gari na watan Fabrairun 2025.

Olaf Scholz yayin ziyararsa a Magdeburg, ya yi Allah wadai da harin da aka kai
Olaf Scholz yayin ziyararsa a Magdeburg, ya yi Allah wadai da harin da aka kaiHoto: Christian Mang/REUTERS

Kasa da sa'a guda bayan harin da aka kai a kasuwar Kirsimeti ta garin Magdeburg da ke Jamus aka fara samun 'yan siyasa da ake gani suna amfani na lamarin wajen karfafa matsayinsu a siyasance tare da yada bayanai marasa tushe bare makama. 'Yan siyasa irin Martin Sellner mai matsanancin ra'ayi na kasar Austria yana kan gaba a nahiyar Turai cikin 'yan siyasa wajen yada bayanai marasa inganci.

Karin bayani: Jamus na tuni da harin kasuwan Krismeti

Sven Tritschler mataimakin bangaren 'yan majalisa na jam'iyyar AfD mai kyamar baki a majalisar dokokin jihar North Rhine-Westphalia wadda take zama jiha mafi yawan mutane a Jamus, ya ce tuntuni jam'iyyarsu ta sallami mutumin da ya kai wannan hari. Shi kuwa Benjamin Höhne da ke zama masanin harkokin siyasa kana mai bincike kan jam'iyyu na ganin haka a matsayin lamarin siyasa da zai kara takura batun samun mafaka ga bakin haure.

" Bayan harin, jagororin AfD suka fara farfaganda a kafofin sada zumunta" - Benjamin HöhneHoto: Ministerium für Inneres und Sport des Landes Sachsen-Anhalt

Höhne ya ce: "Haka abin yake tafiya, ana kara komawa zuwa matsanancin ra'ayi. Bude kofa ga manufofin baki saboda kare hakkin dan Adam abu ne da ya ja-baya. Kuma irin wannan hari na Magdeburg na matse yanayin."

Ita dai jam'iyyar AfD mai kyamar baki tana gani yanayin da milyoyin mutane suke kokarin tserewa daga inda suke rayuwa ne ke kawo matsalolin tsaro a Jamus, kuma sake mayar da milyoyin mutanen inda suka fito shi ne mafita. Ita kanta shugabar jam'iyyar AfD ta kasa kuma 'yar takarar mukamun shugabar gwamnati, Alice Weidel bayan harin da aka kai a Jamus, ta yi wani shagube a shafinta na sada zumunta tana mai cewa "Yaushe wannan wautar za ta kawo karshe" kuma wannan na zuwa jim kadan gabanin zaben kasa baki daya da zai gudana a watan Fabreru na shekarar 2025.

Karin bayani: Yinkurin kai hari a Jamus ya ci tura

'Yan siyasa da dama sun soki Nancy Faeser da ke zama ministar harkokin cikin gida na Jamus saboda gazawa wajen daukan matakan da suka dace, duk da cewa hukumomin Saudiyya sun gargadi mahukuntan Jamus kan wannan mahari. Saboda haka ne Benjamin Höhne, masanin harkokin siyasa kana mai bincike kan jam'iyyu ke ganin cewar 'yan siyasa musamman masu matsanancin ra'ayi za su daura alhakin haka kan gwamnatin tarrayar Jamus

Manyan 'yan takarar shugabancin gwamnatin Jamus na yada manufofinsu kan tsaroHoto: photothek/dpa/picture alliance

Benjamis Höhne ya ce: "Ana iya tunanin cewa duk jam'iyyun siyasa, musamman masu matsanancin ra'ayi, za su nuna tsangwama ga ministar cikin gida da jam'iyyar SPD game da yanayin da ake ciki na tsaro. Saboda jam'iyyar SPD ita ce ke da alhakin kula da ma'aikatar cikin gida gami da tsaron kasa a matakin tarayya, sannan ita kuma za ta yi kokarin kare kanta saboda manufofi a bangaren Magdeburg."

Karin bayani: Jamus: Yiwuwar samun farmakin kyama

Har daga kasashen ketare, akwai masu katsalandan kan zaben Jamus, inda hamshakin mai arziki na Amurka, Elon Musk ya shiga cikin wadanda suka caccaki gwamnatin Jamus bayan harin na garin Magdeburg, har ya bukaci shugaban gwamnati Olaf Scholz da ya ajiye aiki.