Harin mata masu hijabi, kalubale ga mata musulmi
July 29, 2014Kungiyar Mata masu wa'azi wadanda aka fi sani da "Women in Da'a'wah” da malaman addinai a Tarayyar Najeriya sun gargadi Jami'an tsaro da Jama'ar gari game da yiwuwar fara cin mutuncin 'yan mata masu sanya hijabi ko nikafi sakamakon wasu hare-haren da wasu kananan yara mata guda kai a jihar Kano. A wani abin da ake wa kallon sabon salon kai hari.
Yanzu haka dai wannan sabon salon kai farmaki na kunar bakin waken da kananan yara mata 'yan tsakanin shekaru 16 zuwa 17 ke kaiwa sanye da rigar hijabi, ta sanya kungiyoyin mata masu wa'azi a Nigeria fara yin kira ga jami'an tsaro da al'ummar kasar gami da daukar matakan hanyoyin kaucewa cin mutuncin sauran mata da ke sanye da hijabi ko nikafi, don kawar da fitina a cikin kasar.
Malama Hadiza Musa wadda ke daya daga cikin kungiyoyin mata masu wa'azi a Najeriya ta nuna bacin ranta game da yadda wadannan 'yan mata ke shiga irin ta musulunci suna tayar da kayar baya, alamarin da ke nuni da cewa wanan wata hanya ce ta matsawa mata manya da kananan masu sanya Hijibi
Kokarin lalata mana addini ne suke yi, domin babu wanda addinin sa ya tilasta masa ya kashe bawan Allah, tac e suna fakewa ne da sunan addini, kuma suna kokarin lalata mana addinin mu, a saboda haka, muna san su sani da cewa duk wanda ya hallaka wani bawan Allah, to shima ya jira na shi lokacin
A wannan karon dai hatta kungiyar majalisar koli ta tabbatar da shari'ar musulunci a Najeriya da majalisar limamai da alarammomi ta kasa fitowa ne suka yi fili ta kafafen watsa labarai karara suna nuna takaicin su game da wannan batu kamar dai yadda za ku ji daga bakin Dr Baba Ahmed Babban Sakatare Janar na kasa ke cewa
Mata a koina a duniya suna da 'yancin sanya hijabi don kare kansu, domin kowace mace ta na da nata 'yancin da Allah ya bata, wanda kuma tauye mata wannan hakkin, tamkar nuna mata wani wariya ne a cikin alumma, ya ce muna yin kira ga al'ummar kasar wajen sanin cewa, lallai dai kam akwai mutanen kirki ta ko'ina a cikin wannan kasar, haka zalika akwai marasa kirki masu tayar da hankalin al'umma, fatar mu a nan itace hukumomi su yi taka-tsantsan wajan sanin hakkokin mata, da kuma kaucewa musguna masu, don samun dorewar zaman lafiya tsakanin kowa.
Mawallafi: Ibrahima Yakubu
Edita: Pinado Abdu Waba