1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Harin ramuwar gayya ne mafita ga Iran?

Yaya Azare Mahamud ZMA
June 13, 2025

Biyo bayan harin da Isra'ila ta kai wa cibiyoyinta na binciken nukiliya da ya halaka jagororin sojinta, Iran ta kai wa Isra'ila harin ramuwar gayya.

Hoto: TASNIM NEWS/AFP via Getty Images

Biyo bayan hare-haren da Isra'ila ta kai da suka lalata wasu cibiyoyinta na binciken nukiliya da halaka jagororin sojinta, Iran ta kai wa Isra'ila harin ramuwar gayya da daruruwan jirage marasa matuka.

Gidan talabijin kasar ta Iran dai ya nuna yadda wasu jirage masu sarrafa kansu guda dari suka doshi kasar Isra'ila. A yayin da aka kunna na'urorin harba manyan makamai masu linzami da Iran din ke shirin harbawa.

Kuma kamar yadda jagoran addinin kasar ta Iran Ayatollah Khamenei ,wanda ya zargi Amurka da zama kanwa uwar gami a kaiwa kasar tasa hare-haren da Isra'ila tayi ke shan alwashi, hare-haren ramawa kura aniyarta da kasarsa zata kai za su matukar girgiza Isra'ila.

Ajatollah KhameneiHoto: KHAMENEI.IR/AFP

"Manyan makiyanmu Isra'ila da Amurka sun kitsa wannan kisisinar kawo mana hari ne don durkusar da al'ummar Iran. Sun kuma tafka mummunan kuskuren da za su gani a kwaryarsu. Za su san cewa kasar Iran ba kanwar lasa ba ce. Tuni kuma muka maye gurbin jagororinmu baraden da suka yi shahada da wasu makamantansu koma wadanda suka fi su. Babu abun da wadannan hare-haren za su yi wajen rage karkashin kasar Iran da ci gaba da jagorantar ta da kayar baya ga makiyanmu".

Shi ma jakadan kasar ta Iran a MDD, Amir Saeid Iravani ya nemi kasashen duniya da su yi tofin Allah tsine ga hare-haren na Isra'ila kan kasarsa, yana mai bayyana hakkinta na daukar matakan daukar fansa.

"Iran dama a shirye take ta daukar wa kanta fansa ta kuma dakile duk wani yunkurin kai mata wasu hare-haren ta'addancin da Isra'ila ke shirin yi. Dokokin kasa da kasa a yanzu sun bamu cikakken 'yancin daukar matakan ramuwar gayya da koya wa makiyanmu darasin da ba za su taba mantawa dashi ba".

Hoto: MEGHDAD MADADI/TASNIM NEWS/AFP/Getty Images

A kasar ta Iran, yadda dubun dubatan mutane bayan sallar juma'a suka fito dauke da tutar kasar suna kira da a gaggauta daukar fansa, an  kafa jar tuta a masallacin birnin Qum, lamarin da ke alamanta tsundumar kasar ta Iran cikin yakin sai baba ta gani. Kuma kamar yadda Fatima Haidar Jallab, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ke cewa, hare-haren da Iran din zata kaisu kan Isra'ila na karya kashin baya ne.

Jami'an leken asirin Iran sun jima da tara bayanan sirri kan shirin nukiliya Isra'ila, wadanda a yanzu sun zama halatattun wuraren da jamhuriyar musulunci zata dukufa wajen kaiwa hare hare. Har ya zuwa yanzu dai ba a gama tantance irin asarar da hare-haren daren juma,ar da Isra'ilan ta kai a sassa daban daban na kasar ta Iran ba, sai dai kamar yadda firaministan Isra'ila Natenyahu ke ikirari, hare-haren na somin tabi ne, da za su ci gaba da kaisu har sai hakarsu ta cimma ruwa.

Benjamin NetanjahuHoto: MENAHEM KAHANA/AFP

"Hare-harenmu sun yi nasarar ragargaza karfin nukiliya na Iran. Mun halaka manyan malamansu na nukiliya da ke kan gaba wajen gaggauta kammala kera makamin nukiliya. Wadannan hare-hare ne da sai da muka tabbatar da cewa, za su kashe maciji da saren kansa kana muka kaggadamar da su. Mun sha yin alwashin ragargaza karfin nukiliya na babbar makiyarmu yar ta'adda Iran yau kuma sun ga fada da cikawa".