1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin Rasha ya haifar da mace-mace a Ukraine

Mouhamadou Awal Balarabe
August 25, 2022

Makamai masu linzami na Rasha sun kashe mutane 22 a tashar jirgin kasa na birnin Chaplyne da ke gabashin Ukraine. Dama shugaba Zelenskyj ya yi fargabar ganin Rasha ta yi amfani da ranar samun 'yancin kai wajen kai hari.

Ukraine Kiew | Feier Unabhängigkeitstag
Hoto: Metin Aktas/AA/picture alliance

A cewar shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyj, taragogin jirgin kasa guda hudu ne suka kone lokacin da dakarun mamaya na Rasha suka kai wannan harin, yayin da fiye da mutane 50 suka jikkata. A halin da ake ciki dai, Amirka ta yi alkawarin ba da dala miliyan dubu uku don samar da kayan yaki ga gwamnatin Kyiv musamman ma harsasai da kuma horar da sojojin Ukraine.

Dama shugaba Zelenskyj ya yi ta fargabar ganin Rasha ta yi amfani da ranar cika shekaru 31 da samun 'yancin kan Ukraine wajen kai hare-haren rokoki a kan manyan biranen kasar. Selenskyj ya yi kira ga jama'a da su ci gaba da bin dokar hana fita, watannin shida bayan da Rasha ta mamaye kasar.