1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-haren roka ya hallaka farar hula

Abdoulaye Mamane Amadou
March 21, 2021

Luguden wutar da sojoji suka yi a Siriya ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula shida a Lardin Atareb da ke Arewa maso yammacin kasar

Syrien | Angriff auf Krankenhaus in Aleppo
Hoto: Kasim Rammah/AA/picture alliance

Harin ya shafi wani bangare na asibitin lardin ne, kuma baya ga wadanda suka mutu, da akwai wasu mutun fiye da 10 da suka jikkata ciki har da ma'aikatan babban asibtin, in ji hukumar da ke sa ido kan batun kare hakin dan Adam ta kasar.

Wannan lamarin na faruwa ne a yayin da ake ciki yanayi na mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta a yankin, yarjejeniyar da kuma aka yi wa fata na ganin ta kawo maslaha ga kisan kiyashin da lardin ke fama da shi.