1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Harin RSF a yankin Darfur na Sudan ya halaka mutane 12

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
November 2, 2024

Haka zalika harin ya jikkata mutane biyar, sannan kuma dakarun RSF sun yi garkuwa da wasu mutane uku.

Hoto: Volunteer Group South Khartoum Emergency Room/Xinhua/IMAGO

Wani harin da dakarun sa kai na RSF suka kai a yankin Darfur na Sudan ya halaka mutane 12 a Asabar din nan, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Faransa APF ya rawaito.

Haka zalika harin ya jikkata mutane biyar, sannan kuma dakarun RSF sun yi garkuwa da wasu mutane uku.

Karin bayani:Mutane 20 sun halaka sakamakon hari ta sama a Sudan

Tun a cikin watan Afirilun shekarar 2023 yakin basasa kan madafun iko ya barke tsakanin sojojin gwamnati karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan, da kuma dakarun RSF da ke biyayya ga Mohamed Hamdan Dagalo da ake wa lakabi da Hemedti.

Karin bayani:Wani sabon hari a kasuwa ya halaka rayuka a Sudan

Dubban mutane ne suka rasa rayukansu a dalilin yakin, yayin da wasu miliyoyi suka tsere daga gidajensu don tsira da rayukansu.