Amirka ta tuhumi Iran da kaiwa Saudiyya hari
September 15, 2019Tun da fari sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ya dora alhakin hare-haren da aka kaiwa Saudiyya din a dan tsukin nan wanda yawansu ya ki 100 kan kasar ta Iran.
Da ya ke mai da martani game da wannan zargi shugaban dakarun tsaron juyin juya hali a kasar ta Iran Janar Amir Ali Hajizadeha ya gargadi Amirka da cewar jami'an rundunar, sun shirya tsaf don kai harin ramuwar gayya da makamai masu linzami a dukkan sansanin sojin Amirka da ke yankin Gabas ta Tsakiya da zarar Amirka ta kai hari matatun man Iran.
Da yake tsokaci kan wannan batu, ministan harkokin kasashen wajen Birtaniya Dominic Raab ya yi Allah wadai da harin da a ka kaiwa matatar mai a Saudiyya, tare da danganta al'amarin da yunkurin durkusar da hada-hadar mai tsakanin kasashen duniya. Wannan danbarwa dai na zuwa ne yayin da babban taron Majalisar Dinkin Duniya ke gabatowa.