Harin ta'addanci a Bakasin Kamaru
February 12, 2011
Harin ta'addacin da ke zama irinsa na uku cikin mako guda da 'yan tawayen Bakasi na ƙasar kamaru suka kai ya haddasa mutawar mutane biyu. Jami'an sojen ƙasar suka ce wani sojan ƙundun bala ɗaya da kuma ɗan tawaye ɗaya ne dai suka rigamu guidan gaskiya a lokacin musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu. Hukumomin wannan ƙasa ba su bayyana sunan ƙungiyar da ta kai wannan hari ba. Sai dai shugaba Paul ya katse ziyarar aiki da ya ke yi a ƙasashen waje domin gudanar da wani taro na gaggawa da hafsoshin sojen ƙasar.
Manyan jami'an gwamnati da ke aiki a tsibirin har guda13 ne, 'yan tawayen ke garkuwa da su a halin yanzu da nufin samun diyya. Ana ci gaba da fiskantar tabarbarewan matakan tsaro a yankin mai arzikin man fetur da kuma kifi, wanda kotun ƙasa da ƙasa da mallaka wa Kamaru bayan shekaru tana taƙaddama akan tsibirin da makobciyarta wato Najeriya. 'Yan tawayen na neman hukumomi su gaggauta gudanar da ayyukan gina ƙasa a yankin. Yayin da wasun daga cikin ƙungiyoyin 'yan tawayen ke ci gaba da adawa da kasancewa ƙarƙarshin mulkin Kamaru.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu