Harin ta'addanci a Mali ya halaka mutane fiye da 50
May 7, 2026
Kimanin mutane fiye da 50 ne suka mutu a Mali, sakamakon hare-haren ta'addanci na kungiyar JNIM mai alaka da Al-Qaeda, a kauyukan Korikori da Gomossogou na kasar, kamar yadda wani jami'in gwamnatin kasar ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP.
To sai dai wata hadakar kungiyar 'yan jarida ta WAMAPS, mai bibiyar al'amuran da ke wakana a yankin Sahel, ta ce alkaluman mamatan ka iya karuwa.
karin bayani: MDD ta zargi yan awaren Azawad na Mali da kashe fararen hula
Kungiyar ta kara da cewa wasu mutane da dama sun bace, ba a kai ga gano inda suka nufa ba, kuma an sace wa mutanen kauyukan kadarorinsu sannan aka kona wasu.
Karin bayani: Sharhi kan yadda makomar Mali za ta kasance
A na ta bangaren, gwamnatin mulkin sojin Mali ta ayyana samun nasarar halaka 'yan ta'adda da dama, bayan yi musu kawanya a maboyarsu, to sai dai babu wani karin haske da ta bayar a kai.
Karin bayani:Ko harin Mali zai zama ishara ga Nijar?
Hare-haren ta'addanci na kawancen kungiyar 'yan awaren Azawad da JINIM, a ranakun 25 da kuma 26 na Afirilu su ne suka yi sanadiyyar mutuwar ministan tsaron Mali Sadio Camara a birnin Bamako.