SiyasaAfirka
Harin 'yan bindiga a Burkina Faso ya halaka mutane da dama
February 26, 2024![](https://static.dw.com/image/63310558_800.webp)
Talla
Wani harin ta'addanci a masallaci da coci a kasar Burkina Faso ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da har yanzu ba a san adadinsu ba, kamar yadda kamfanin dillancin Faransa AFP ya rawaito.
Karin bayani:Burkina Faso: Dakile yunkurin tada zaune tsaye
Wani jami'in tsaron kasar ya ce maharan sun dirar wa wani masallaci lokacin da ake sallar asuba a Lahadin nan, sannan suka bude wa masallatan wuta suka kashe su har da limaminsu.
Karin bayani:Mali da Burkina Faso da Niger sun lashi takobin karfafa hulda
Yayin da kuma dai a Lahadin 'yan bindigar suka far wa wata mujami'a tare da kashe masu bauta 15 sannan suka raunata mutane biyu.