1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Harin ta'addanci a Pakistan ya halaka mutane kusan 30

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 7, 2024

Kamfanin dillancin labaran Jamus DPA ya rawaito cewa harin farko ya faru ne a lardin Balochistan, inda ya halaka mutane 14 da jikkatar wasu 30

Hoto: Banaras Khan/AFP

Hare-haren ta'addanci a lokuta daban-daban yau a Pakistan, sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 26 tare da jikkata sama da 30, gabanin babban zaben kasar da za a gudanar ranar Alhamis.

Karin bayani:Harin ta'addanci ya halaka 'yan sandan Pakistan 10

Wani jami'in gwamnatin kasar Jamal Uddin ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Jamus DPA cewa harin farko ya faru ne a a lardin Balochistan mai fama da rikici, inda jami'in 'dan sandan kasar Ikhtiar Mohamed ya tabbatar da mutuwar mutane 14 da jikkatar wasu 30, bayan 'dana bam a wurin ajiye babura da ke ofisihin 'dan takarar majalisar yankin.

Karin bayani:Hukumar zabe ta tuhumi tsohon fraministan Pakistan

Na biyun kuma ya tashi ne a kusa da ofishin 'dan takarar majalisar yankin Qila Saifullah, in ji jami'in 'dan sanda Mohamed Sabir, inda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 12 da jikkata wasu da dama.