Burkina Faso: Hari ya halak sojoji
April 28, 2023Talla
Rundunar sojojin Burkina Fason da ta tabbatar da afkuwar lamarin, ta bayyana cewa an kai mata harin ne a Alhamis din wannan mako a garin Ouagarou da ke gundumar Gourma. Rundunar da ta bayyana hakan cikin wata sanarwa, ta kuma kara da cewa sojojin a nasu bangaren sun samu nasarar halaka mayakan masu ikirarin jihadi 40. Tsawon shekaru bakwai ke nan da mayakan masu alaka da kungiyoyin 'yan ta'adda na al-Qaida da IS, suka addabi Burkina Faso da hare-haren da aka kiyasta sun halaka dubban mutane tare da tilasta kimanin miliyan biyu kauracewa gidajensu.