1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mayakan ISWAP sun halaka mutane 59

Binta Aliyu Zurmi
June 10, 2020

A Najeriya mayan kungiyar ISWAP sun kai wani mumunar hari a wani kauye na Felo da ke da tazarar kilomita 80 da fadar gwamnatin Jihar Borno a shiyar arewa maso gabashin Najeriya wanda yai sanadiyar mutuwar mutane 59.

Nigeria Baga | Truck des IS Gruppe (ISWAP)
Hoto: Getty Images/AFP/A. Marte

Al'umma mazauna yankin da 'yan kato da gora da ake kira  JTF sun tabbatar wa da kamfanin dillancin labarai AFP mallakar Faransa aukuwar wannan harin. Mayakan na Iswap sun shiga kauyen ne a babura dauke da manyan bindigogi suna harbi kan mai uwa da wabi, da tarwatsa mutane gami da bi ta kansu da ababben hawansu. Shugaban rundunar JTF masu yaki da 'yan bindiga Babakura Kolo ya tabbatar da gano gawawaki 59. Ayyukan ta'addanci a yankin arewa maso gabashin kasar ta Najeriya sun yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da dubu 36 ya yin da sama da mutum miliyan biyu rasa matsuguninsu.