1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Harin ta'addanci ya halaka mutane 39 a Jamhuriyar Nijar

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 16, 2024

Ma'aikatar tsaron kasar ta ce maharan sun far wa yankunan Kokorou da Libiri da ke kan iyakarta.

Hoto: AFP

Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta tabbatar da mutuwar mutane 39 da suka da hada da mata da kananan yara, sakamakon hare-haren ta'addanci biyu a yammacin kasar.

Karin bayani:Kulla alakar tsaro tsakanin Chadi da Nijar

Ma'aikatar tsaron kasar ta ce maharan sun far wa yankunan Kokorou da Libiri da ke kan iyakarta, to sai dai ba ta yi wani karin haske kan lokutan da aka kai hare-haren ba.

Karin bayani:'Yan ta'adda sun kona ofishin likitocin agaji a Burkina Faso

Jamhuriyar Nijar tare da makwabtanta Mali da Burkina Faso, na daga cikin kasashen yankin Sahel da ke fama da ayyukan ta'addanci tun cikin shekarar 2012 zuwa yanzu, lokacin da masu gwagwarmaya da makamai da ke da alaka da al-Qaeda suka kwace iko da wasu sassan kasar Mali.