1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Ta'addanci

Harin ta'addanci ya halaka sojoji a Burkina Faso

Binta Aliyu Zurmi SB
September 25, 2022

Mutane hudu da suka hada da jami'an tsaro biyu sun rasa rayukansu sakamakon harin ta'addanci a kasar Burkina faso da ke yankin yammacin Afirka.

Burkina Faso - Denkmal in Ouagadougou
Hoto: imago/ZUMA Press

Rahotanni daga Ouagadougou na cewar wani harin ta'addanci ya hallaka jami'an tsaro hudu a gabashin kasar Burkina Faso a yayin wani aikin sintirin tsaro da suke yi tsakanin garuruwan Sakoani da Sampieri a yankin Tapoa mai makwabtaka da kasashen Jamhuriyar Nijar da Jamhuriyar Benin.

Harin kwantan baunar na 'yan ta'addan ya halaka sojoji biyu da kuma wasu biyu daga tawagar masu rajin kare kasarsu ta kungiyar VDP.

Wata majiya ta tabbatar da samu asarar rayuka a bangaren 'yan ta'addan a gumurzun da suka yi.

Tun a shekarar 2015 Burkina Faso ke fama da da mayankan da ke ikirarin jihadi, wanda ya yi sanadiyar rayukan dubban mutanen  tare ma da raba sama da miliyan biyu da matsugunansu.

Ire-iren wadannan hare-haren a kan jami'an tsaro da farafen hula da masu bada agaji na kara karuwa a kasar da ke fama da matsalar tsaro da kuma ta shugabanci.