1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Harin ta'addanci ya halaka 'yan sandan Pakistan 10

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 5, 2024

Wani jami'in 'dan sandan kasar mai suna Malik Anees ul Hassan, ya shaidawa Reuters cewa maharan masu yawan gaske, sun fara amfani da bindigogi ne sannan daga bisani suka rinka jefa gurneti da hannu kan jami'an na su

Hoto: AFP

Wani harin ta'addanci da asubahin Litinin din nan a Pakistan ya halaka 'yan sandan kasar 10 tare da jikkata wasu 6, bayan da maharan suka kutsa kai cikin ofishin 'yan sandan a yankin Draban na arewacin kasar.

Karin bayani:Pakistan: Kotu ta yankewa Imran Khan hukuncin dauri

Wani jami'in 'dan sandan kasar mai suna Malik Anees ul Hassan, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa maharan masu yawan gaske, sun fara amfani da bindigogi ne sannan daga bisani suka rinka jefa gurneti da hannu kan jami'an na su.

Karin bayani:Hukumar zabe ta tuhumi tsohon fraministan Pakistan

Harin dai na zuwa ne kwanaki kadan gabanin gudanar da babban zaben kasar. Ko a cikin watan Disamban bara wani harin kunar bakin wake ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin Pakistan 23.