1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Harin Tel Aviv ya kashe mutum guda da raunata wasu 10

Zainab Mohammed Abubakar
July 19, 2024

'Yan Houthi na kasar Yemen sun dauki alhakin harin da jirgin sama mara matuki ya kai a birnin Tel Aviv, inda 'yan sanda suka ce ya zuwa yanzu an samu gawar mutum guda.

Hoto: Gil Cohen-Magen/AFP/Getty Images

Sanarwar da 'yan tawayen suka fitar, wadanda suka kai hare-hare da dama kan jiragen ruwa masu dakon kaya a teku, na cewar harin wani mataki na nuna goyon baya ga Falasdinawa ayakin Gaza. Dakarunsu na UAV sun aiyana kai harin a daya daga cikin muhimman wurare a yankin Jaffa da Isra'ilar ta mamaye, wanda a yanzu ake kira Tel Aviv a Isra'ila."

Da sanyin safiyar Juma'ar nan ce dai, aka ji karar fashewar wani abu a kan titunan tsakiyar birnin na Tel Aviv, wanda ya raunata a kalla mutane 10, ya kuma yi sanadiyyar mutuwar mutum guda.

Sojojin Isra'ila sun ce suna nazarin wannan harida kuma kara sintiri ta sama bayan afkuwar lamarin, wanda binciken farko ya gano cewa wani hari ne da aka kai ta sama.