Harin tsageru ya hallaka fiye da mutane 10 a Somaliya
November 1, 2015Rahotanni sun nuna cewa fiye da mutane 10 sun hallaka sakamakon harin 'yan bindiga na kungiyar al-Shabaab a wani otel da ke birnin Mogadishu fadar gwamnatin Somaliya da safiyar wannan Lahadi. Kungiyar ta al-Shabaab wadda take da alaka da al-Qaeda ta dauki alhakin harin kan wannan otel da ke da baki manyan ma'aikatan gwamnati da 'yan kasuwa.
Shaidun gani da ido sun ce an samu fashewar daga cikin wata mota da tsagerun suka yi amfani da ita a kofar wannan otel. Tuni dakarun kiyaye zaman lafiya na kungiyar Tarayyar Afirka suka bayyana samun nasarar dakile tsagerun maharan. Akwai kimanin dakarun na kiyaye zaman dubu 22 a kasar ta Somaliya mai fama da tashe-tashen hankula, wadanda suke taimakon jami'an tsaron gwamnati wajen aikin samar da zaman lafiya.