Kwango: An halaka jakadan kasar Italiya
February 22, 2021Hukumomin Kwango sun tabbatar da mutuwar jakadan kasar Italiya da wasu mutum biyu a sakamakon wani hari da ake zargin na kwanton bauna ne, da aka kai kan wani ayarin motocin jami'an Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya a yankin wato World Food Programme (WFP) a Goma na jamhuriyyar ta Kwango mai fama da rikici. Gwamnatin Italiyan, ta tabbatar da labarin mutuwar jakadan mai suna Luca Attanasio, sanarwar ta ce ya mutu ne a wani asibiti da ke birnin Kinshasa a sakamakon raunin da ya ji daga harin.
Attanasio, yana da shekaru 43 a duniya, ya kuma soma aikin jakadancin ne tun daga shekarar 2017, baya ga Kwango yayi aiki a Moroko da Najeriya a matsayin jakadan Italiyan. Shugaban kasar Italiya Sergio Mattarella, yayi alla-wadai da harin da ya kira irin na ragwaye. A nata bangaren, rundunar sojin Kwango ta ce ta kaddamar da samame don gano wadanda suka kai harin na wannan Litinin.