1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin 'yan ta'adda ya hallaka ministan tsaron Mali

Binta Aliyu Zurmi
April 26, 2026

Harin kawance na 'yan ta'adda da 'yan tawaye Azbinawa da suka kai a Bamako da wasu biranen Mali ya yi sanadiyar mutuwar ministan tsaron kasar Sadio Camara a gidan shi dake Kati.

Mali Der neue Verteidigungsminister Sadio Camara
Hoto: Boubou Doucouré, Pressedienst des Premierministers

Harin wanda jami'an sojin suka tabbatar da murkushe shi, sai dai da safiyar wannan rana an sake jiyo amon harbin bindiga da aka tabbatar da barkewar fada a garin na Kati, tungar mulkin Mali.

'Yan tawayen Abzinawa sun sanar da yarjejeniyar da za ta bai wa sojojin Rasha damar ficewa daga garin Kidal da ke arewacin kasar, wanda suka yi ikirarin cewa yana karkashin ikonsu gaba daya.

 

Karin Bayan Yan awaren Azawad na Mali sun yi ikirarin kwace iko da Kidali :