1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Taron APC ya tsayar da harkoki

Uwais Abubakar Idris
March 27, 2026

Matakin tilasta rufe sakatriyar gwamnatin tarayyar a Najeriya saboda babban taron jam'iyyar APC mai mulki da ake gudanarwa a Abuja, ya dakatar da aiki tare da sanya ma'aikatan gwamnati sama da dubu 720 zama a gida.

Jam'iyyar APC a Najeriya
Jam'iyyar APC a NajeriyaHoto: SAMUEL ALABI/AFP

Daukacin hanyoyin da suka nufi tsakiyar birnin Abuja zuwa dandalin da ake gudanar da wannan taron an rufe su kirif, inda motocin da ke da izini ne kadai ke da ikon ratsawa. Wannan ya tilasta an bai wa ma'aikatan gwamnati da ofisoshinsu ke a babbar sakatariya, umurnin su zauna gida. Matakin da  gwamnatin Najeriyar ta dauka saboda babban taron na jam'iyyar APC mai mulki, ya shafi ma'aikata gwamnati har ma da na wasu kamfanonin 'yan kasuwa.

Najeriya: Atiku Abubakar ya koma ADC

01:25

This browser does not support the video element.

A bisa al'ada jam'iyyun siyasa a Najeriyar kan gudanar da manyan tarurrukansu a ranakun karshen mako ne, domin kaucewa kawo cikas ga aikin gwamnati da ma kai da komowar jama'a  saboda kusancin dandalin da ake gudanar da taron da babbar sakatariyar ma'aikatan gwanati.  Kwararu a fanin tsare-tsaren tattalin arziki a Najeriyar na bayyana cewa, lokaci ya yi da kasar za ta tsara yadda za a kaucewa kawo cikas ga ayyuka da harkokin kasuwanci a lokutan irin wadannan tarurruka da ma zabe.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani