1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harkokin siyasa ba bisa doka ba a Masar

February 8, 2012

Masar ta zargi wasu kungiyoyi da saɓawa doka wajen gudanar da harkokin siyasa

Workers from a non-governmental organization National Democratic Institute, or NDI, wait as Egyptian officials raid their office in Cairo, Egypt, Thursday, Dec. 29, 2011. Egyptian soldiers and police stormed non-governmental organization offices throughout the country on Thursday, banning employees inside from leaving while they interrogated them and searched through computer files, an activist and security official said. (Foto:Mohammed Asad/AP/dapd)
Wasu kungiyoyin agaji a MasarHoto: dapd

Wasu alƙalan dake binciken zargin da ake yiwa wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu na samun kuɗaɗen shiga ta hanyar da bata dace ba daga ƙetare, a wannan Larabar sun zargi ƙungiyoyin da gudanar da harkokin siyasar da suka saɓawa dokokin ƙasar ta Masar. Alƙalan sun bayyana hakan ne domin kare matakin da suka ɗauka na gurfanar da wasu wakilan irin waɗannan ƙungiyoyin a gaban shari'a. A lokacin daya ke yiwa manema labarai jawabi, wani alƙali a Masar Sameh Abu Zeid, ya ce ƙungiyoyin da ake binciken suna gudanar da harkokin su ne ba tare da izinin hukuma ba, kana ayyukan da suke gudanar wa sun shafi na siyasa ne tsantsa, wanda kuma ba shi da wata alaƙa da aikin ƙungiyiyoyin fararen hula.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu