Harkokin siyasa na fuskantar koma baya a Kenya
January 1, 2008Talla
´Yan sanda a Kenya, na ci gaba da arangama da matasa, ma su zanga-zangar adawa da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa, daya bawa Mwai Kibaki nasara. A yanzu haka dai mutane sama da ɗari sun rasa rayukansu, a sakamakon wannan fito na fiton. Mahukunta sun ce tuni aka sa dokar ta ɓaci a garin Kisumu, don tabbatar da doka da oda. Rahotanni sun tabbatar da bawa ´yan sanda umarnin harbe duk wanda ya ƙarya wannan doka. Mr Raila Odinga, daya sha kaye a zaɓen na shugaban ƙasa ya buƙaci ´yan ƙasar yin adawa da sakamakon zaɓen. Jam´iyyun adawa na ƙasar sun zargi Gwamnati da sace wannan zaɓe ta hanyar yin maguɗi. Tuni dai Mwai Kibaki ya karɓi rantsuwa, a matsayin tazarce na tsawon shekaru biyar a karo na biyu a jere.