Harkokin zabe a kasar Venezuela
December 3, 2006Miliyoyin mutane da suka can can ci yin zabe a kasar Venezuela na ci gaba da kada kuri´un su, don zabar shugaban kasa.
Shugaba Hugu Chavez, wanda ke adawa da Amurka, kuma daya daga cikin yan takarar, a yanzu haka akwai kyakkyawan zaton cewa shine zai lashe zaben, don sake wa´adi na shekaru shida a madafun ikon kasar.
Rahotanni dai sun rawaito mai adawa dashi, wato Mr Manuel Rosales na cin alwashin samun nasarar wannan zabe, akan abokin karawar tasa, daya soka a matsayin mai mulkin gurguzu irin na kasar Cuba.
Bayanai dai sun shaidar da cewa Mr Rosales, na da ra´ayi ne na daidai ta harkokin kasuwa a kasar , idan ya dare madafun ikon.
Shi kuwa Hugu Chavez, mutum ne dake da karbuwa a tsakanin talakawa da kuma ma´aikata a kasar, wadanda ke goyon bayan shirin sa na kawar da talauci.