1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Harris na zawarcin kuri'un musulmi a Michigan

October 4, 2024

A ci gaba da neman kuri'un Amurkawa Musulmi, mataimakiyar shugabar kasar da ke takara a jam'iyyar Democrats Kamala Harris ta isa Michigan domin neman kuri'ar Amurkawan da ke tsatso da Larabawa.

Mataimakiyar shugabar Amurka Kamala Harris
Mataimakiyar shugabar Amurka Kamala Harris Hoto: Saul Loeb/AFP/Getty Images

Harris za ta kuma gana da shugabannin kungiyar 'yan Lebanon mazauna Amurka da Hala Hijazi wadanda suka rasa da dama daga cikin 'yan uwansu a yankin Gaza.

Karin bayani: Kalubalen da ke gaban Harris na yin nasara a zaben Amurka

Gabanin ganawar Harris da Musulmin na Michigan, babban mashawarcinta kan tsaro Phil Gordon ya shaida wa al'ummar musulmin cewa gwamnatin Amurka ta damu matuka wajen ganin an kawo karshen yakin Gaza da kuma samar da maslaha ta diflomasiyya a Lebanon har ma da bukatar zaman lafiyar Gabar Yamma da Kogin Jordan.